Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cik…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cik…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda y…
عن أبي بَكرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إِذَا الْتَقَى الْمُسْلِمَانِ بِسَيْفَيْهِمَا فَالْقَاتِلُ وَالْمَقْتُولُ فِي النَّارِ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ هَذَا الْقَاتِلُ، فَمَا بَالُ الْمَقْتُولِ؟ قَالَ: «إِنَّهُ كَانَ حَرِيصًا عَلَى قَتْلِ صَاحِبِهِ».
Bayanin hadisin: Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda y…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana nufin kashe abokinsa, to, mai kisan yana cikin wuta saboda kashe abokinsa, sahabbai suka rikita ga wanda aka kashe; Ta yaya zai zama a wuta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa shi ma yana wuta don kwaɗayinsa a kan kashe ɗan uwansa, babu abin da ya hanashi kisan sai gaggawar mai kisan da kuma rigayarsa da yayi.
Koyarwar hadisin: Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda y…
- Cancantar ukuba a kan wanda ya yi ƙudiri a kan saɓo da zuciyarsa, kuma ya aikata sabubbansa.
- Gargaɗi mai tsanani daga rigima tsakanin musulmai, da narko na wuta mai tsanani a kansa.
- Yaƙi tsakanin musulmai da gaskiya ba ya shiga cikin narkon, misalin yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata.
- Mai aikata babban laifi ba ya kafirta saboda aikata saɓon; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambaci masu yakin (da) musulmai.
- Idan musulmai suka haɗu ta kowace sila ce a ka yi yaƙi a cikinta, sai ɗayansu ya kashe ɗayan, to, wanda ya yi kisan da wanda a ka kashe suna cikin wuta, ambaton takobi a cikin hadisin ta hanyar misaltawa ne.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· AYYUKAN ZUKATA
· ZARGIN AYYUKAN SAƁO
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa