Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wa…

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wa…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ اللهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ يَسَّرَ اللهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَاللهُ فِي عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ، وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللهُ لَهُ بِهِ طَرِيقًا إِلَى الْجَنَّةِ، وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللهِ يَتْلُونَ كِتَابَ اللهِ وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ إِلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمِ السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ، وَحَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ، وَذَكَرَهُمُ اللهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ، وَمَنْ بَطَّأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ».

Bayanin hadisin: Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sakamakon musulmi a wurin Allah yana daga jinsin abinda musulmi yake aikata shi ne tare da musulmai; wanda ya yaye ya gusar ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki da tsanani daga baƙƙan cikin duniya, Allah Zai yi masa sakayya da cewa Zai Yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar alƙiyama. Wanda ya yalwatawa wanda ke ciki matsi ya kuma sawwaƙa masa ya gusar da matsinsa, Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira. Wanda ya suturta wani musulmi kamar idan ya tsinkaya daga gare shi akan abinda bayyanar da shi ba ya kamata na tuntuɓe da kurakurai, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana kasancewa Mai taimako ga bawanSa, muddin dai bawan ya kasance mai tafiya ne akan taimakon ɗan uwansa a maslahohinsa na Addini da duniya, taimako yana kasancewa ne da addu'a da jiki da dukiya da kuma wanin hakan. Wanda ya yi tafiya zuwa tabbatar da wani ilimi na shari'a, yana mai nufin fuskar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi; to Allah Zai sawwaƙa masa hanya zuwa aljanna da shi. Wasu mutane ba su taba taruwaba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah (Msallatai), suna karanta littafin Allah kuma suna mudarasarsa a tsakaninsu, sai nutsuwa ta saukar musu, rahamar Allah ta gamesu ta lulluɓesu, kuma mala'iku sun kewayesu, Allah Ya yi yabo a garesu a cikin makusantan dake wajenSa, kuma ambatan Allah ga bawa a cikin jama'a maɗaukaka ya isa ɗaukaka. Wanda aikinsa ya kasance tauyayye ne, ba zai riskar da shi da darajar ma'abota ayyuka ba, to yana kamata kada ya dogara akan matsayin danganta da falalar iyayeba, ya taƙaita a aiki.

Koyarwar hadisin: Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin…

Rukunan : FALALOLI · FALALAR ILIMI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah