Kowa ne aikin alheri sadaka ne
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Kowa ne aikin alheri sadaka ne
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya ruwaito shi daga hadisin Jabir, kuma Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Huzaifa
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Kowa ne aikin alheri sadaka ne
عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «كُلُّ مَعْرُوفٍ صَدَقَةٌ».
Bayanin hadisin: Kowa ne aikin alheri sadaka ne
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin kyautatawa da amfani ga wasu na magana ne, ko na aiki yana zama sadaka, kuma a cikinsa akwai lada da sakamako.
Koyarwar hadisin: Kowa ne aikin alheri sadaka ne
- Lallai sadaka ba ta taƙaituwa a abin da mutum yake fitar da shi daga dukiyarsa, kai, yana tattaro kowane alherin da mutum zai aikatashi, ko ya faɗeshi ya sadar da shi zuwa wasu.
- A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan yin aikin alheri da dukkanin abin da a cikinsa akwai amfani ga wasu.
- Rashin wulaƙanta wani abu daga aikin alheri ko da ya zama ƙarami ne.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN AYYUKA NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa