Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar d…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar d…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkir…
عن أنس بن مالك رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ أَحَبَّ أَنْ يُبْسَطَ لَهُ فِي رِزْقِهِ، وَيُنْسَأَ لَهُ فِي أَثَرِهِ، فَلْيَصِلْ رَحِمَهُ».
Bayanin hadisin: Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkir…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana kwaɗaitarwa a kan sa da zumuncin 'yan uwa ta hanyar ziyara da girmamawar jiki da dukiya da makamancin hakan, kuma cewa su sababi ne a yalwatar arziki da tsawon rai.
Koyarwar hadisin: Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkir…
- (Abokan) Zumunci su ne 'yan uwa ta ɓangaren uba da uwa, a duk lokacin da ya kasance mafi kusa, to, ya zama mafi cancanta da sadarwa.
- Sakamako yana kasance ne daga jinsin aikin da aka yi, wanda ya sadar da zumuncinsa da kirki da kyautatawa, Allah Zai sadar da shi a rayuwarsa da arzikinsa.
- Sadar da zumunci sababi ne na yalwar arziki, kuma sababi ne na tsawon rayuwa, duk da cewa ajali da arziki abin iyakancewa ne, sai dai cewa zai iya zama albarka cikin arziki da rayuwa, sai ya yi aiki a rayuwarsa mafi yawa kuma mafi amfani daga abin da waninsa zai aikata, a wata faɗar aka ce ƙarin arziki da rayuwa ƙari ne na haƙiƙa. Allah ne Mafi sani.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN AYYUKA NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad