Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mi…

Bayanin hadisin: Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mi…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar akan barin salati gare shi a halin jin sunansa ko alkunyarsa ko siffarsa, ya ce: Marowaci mai cikakkiyar rowa (shi ne) wanda aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba; hakan saboda wasu al'amura:

Na farko: Cewa hakan rowa ce, da wani abun da ba ya asara saboda shi kaɗan ne ko mai yawa, kuma ba ya bada wata dukiya, kuma ba ya yin wani ƙoƙari.

Na biyu: Cewa shi ya yi wa kansa rowa kuma ya haramta mata ladan salati ga Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi haƙiƙa ya yi rowa saboda hanuwarsa daga salati gare shi, kuma ya hanu daga bada haƙƙin da bada shi ya wajaba akansa dan ruko da umarni kuma ake samun lada da shi.

Na uku: Cewa salati gare shi a cikinsa akwai bada haƙƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, shi ne wanda ya sanar damu, kuma shi ne wanda ya shiryar damu, shi ne wanda ya kiramu zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - kuma ya zo mana da wannan wahayin, da kuma wannan shari'ar, shi ne sababin shiriyarmu - bayan Allah - alhrerinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - wanda bai yi masa salati ba zai zama haƙiƙa ya yi wa kansa rowa, kuma ya yi rowa ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani haƙƙin da yana daga mafi ƙasan haƙƙoƙinsa.

Koyarwar hadisin: Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mi…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah