Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama
Bayanin hadisin: Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.
Koyarwar hadisin: Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama
- Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
- Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
- Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
- Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· SABABAI NA AMSAR ADDU'A DA MASU HANA AMSARTA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah