An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe han…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe han…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai…
Bayanin hadisin: An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai…
Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.
Koyarwar hadisin: An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai…
- Sindi ya ce: A taƙaice cewa kowane mutum daga waɗannan haƙiƙa ya samu abinda da badan kasawa daga gare shi ba da ya sami wani rabo mai yawa na alheri, yayin da ya kasa har hakan ya wuce shi to haƙiƙa ya taɓe kuma yayi hasara.
- Kwaɗaitarwa akan salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duk lokacin da aka ambaci sunansa.
- Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari da zage damtse ga ibada a cikin watan Ramadan.
- Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari a cikin biyayya ga mahaifa da kuma girmamasu, musamman ma a lokacin tsufa.
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa