Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي مسعود رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «مَنْ قَرَأَ بِالْآيَتَيْنِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ الْبَقَرَةِ فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ».
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka
Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ZIKIRAN SAFIYA DA YAMMA · FALALOLI NA SURORI DA AYOYI · FALALOLI DA LADUBBA