a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 4

Rubutun hadisin: a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangij…

Bayanin hadisin: a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangij…

Lokacin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukarwa AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne} halitta da mulki, da tasarrufi da jujjuya al'aura, {idan kuka bayyanar} kuka bayyanar kuka nuna {abin da ke cikin rayukanku} da ƙirazanku {ko kuka ɓoye shi} sai kuka ɓoyeshi a cikin zukatanku {Allah zai yi muku hisabinsa} a ranar alƙiyama. {Yana yin gafara ga wanda Yake so} da falalarSa da kuma rahamarSa, {Kuma Yana azabtar da wanda Yake so} da adalcinSa, {Allah Mai iko ne akan dukkan komai} wani abu ba ya gajiyar da Shi. Lokacin da sahabbai suka ji ta sai hakan ya yi musu tsanani; domin a cikinta akwai kama mutum har da abin da ke cikin zuciya na tinanika. Sai suka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, kafin haka an ɗora mana ayyuka na jiki da zamu iya zuwa da shi; misalin sallah da azimi da jihadi da sadaka, sai dai haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma mu ba zamu iyata ba. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce da su: Shin zaku faɗi irin abin da Yahudawa da Nasara suka faɗa: {Mun ji mun saɓa}? Kawai ku ce: {Mun ji mun bi gafararKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa}, sai sahabbai suka amsawa umarnin Allah da ManzonSa, sai suka ce; Mun ji mun bi gafrarKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa. Yayin da musulmai suka faɗeta da harsunansu, kuma rayukansu suka miƙa wuya gareta; sai Allah Ya saukar da tsarkakewa ga Annabi da kuma al'ummarsa da faɗinSa; {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa muminai ma haka} harsunansu da zukatansu suka miƙa wuya gareta. {Kowannen su ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da litattafanSa, da ManzanninSa, bamu banbancewa tsakanin wani daga cikin ManzanniSa}. Kai muna imani da su baki ɗaya {Suka ce Mun ji } faɗinKa {kuma mun bi} umarninKa, muna neman {gafararKa ya Ubangijinmu} da rangwaminKa, {makoma tana wurinKa} da makoma ranar da hisabi zai tsaya, yayin da suka aikata haka, kuma suka faɗi abin da aka umarce su da faɗinsa na bayyanar da ji da kuma bi ga umarnin Allah; sai Allah Yayi sauƙi ga wannan al'ummar Ya shafe waccar ayar da faɗinSa: {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya} da ikonta da kuma ƙoƙarinta, {tana da} ladan {abin da ta aikata} na alheri, {kuma a kanta akwai} uƙubar {abin da ta aikata} na zunubi da laifi, kuma Allah ba Ya kama wani da laifin waninSa, haka da abin da zuciyarsa ta yi wasuwasi da shi. {Ya Ubangijinmu kada Ka kamamu} ka yi mana uƙuba {idan muka manta} bamu tuna ba, {Ko muka yi kuskure} sai muka bar daidai bada gangan ba, sai Allah Ya amsa musu hakan sai Ya ce: Haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana wani nauyi} da wahala da nauyi {Kamar yadda Ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} daga Banu Isra'il da wasunsu, sai Allah Ya amsa kuma Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana abin da bamu da ikon yin sa} na abubuwan taklifi da bala'i da al'amuran da muke gajiyawa daga ɗaukarsu, Allah Ya ce: Eh haƙiƙa na aikata, {Ka yi mana afuwar} zunubanmu Ka shafe mana su, {Ka gafarta mana} zunubanmu Ka suturta mana su, Ka yafe mana su, {Ka yi mana rahama} da rahamarKa yalwatacciya, {Kaine Majiɓincin al'amuranmu} kuma shugabanmu; {To Ka taimake mu} ta hanyar tsaida hujja da rinjaye {Akan mutane kafirai} a yaƙarsu, sai Allah Ya yi musu, sai Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata.

Koyarwar hadisin: a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangij…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · FALALOLI NA SURORI DA AYOYI · TAFSIRIN AYOYI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah