Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (A…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (A…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a…
Bayanin hadisin: Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda gashin kansa a cukurkuɗe yake, ya yi ƙura, ba ya shafa masa mai, kuma ba ya yawan wanke shi, ba shi da wata daraja a wurin mutane dan haka suke ture shi a bakin ƙofofinsu, suna korarsa dan wulaƙanta shi; saidai cewa shi da ace zai yi rantsuwa akan faruwar wani abu da Allah Ya farar da abun, dan girmama shi da amsa roƙonsa, da kuma kiyaye shi daga warware rantsuwarsa, hakan saboda falalarsa da matsayinsa a wurin Allah.
Koyarwar hadisin: Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a…
- Allah ba Ya duba zuwa surorin bawa saidai Yana duba zuwa zukata ne da ayyuka.
- Ya wajaba akan mutum ya kula da aikinsa da tsarkin zuciyarsa sama da kulawarsa ga jiinsa da tufafinsa.
- Kanƙar dakai ga Allah da miƙa wuya gare shi to hakan sababi ne na amsa addu'a, saboda haka; Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana kuɓutar da rantsuwar masu tsoronSa ɓoyayyu.
- Bayanin tarbiyyar Annabi ga mutane; dan kada sashinsu su wulaƙanta sashi.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN AYYUKA NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah