Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka…

عن أبي هريرة رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فِيمَا يَحْكِي عَنْ رَبِّهِ عَزَّ وَجَلَّ، قَالَ: «أَذْنَبَ عَبْدٌ ذَنْبًا، فَقَالَ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي، فَقَالَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَذْنَبَ عَبْدِي ذَنْبًا، فَعَلِمَ أَنَّ لَهُ رَبًّا يَغْفِرُ الذَّنْبَ، وَيَأْخُذُ بِالذَّنْبِ، ثُمَّ عَادَ فَأَذْنَبَ، فَقَالَ: أَيْ رَبِّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي، فَقَالَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: عَبْدِي أَذْنَبَ ذَنْبًا، فَعَلِمَ أَنَّ لَهُ رَبًّا يَغْفِرُ الذَّنْبَ، وَيَأْخُذُ بِالذَّنْبِ، ثُمَّ عَادَ فَأَذْنَبَ، فَقَالَ: أَيْ رَبِّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي، فَقَالَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَذْنَبَ عَبْدِي ذَنْبًا، فَعَلِمَ أَنَّ لَهُ رَبًّا يَغْفِرُ الذَّنْبَ، وَيَأْخُذُ بِالذَّنْبِ، اعْمَلْ مَا شِئْتَ فَقَدْ غَفَرْتُ لَكَ».

Bayanin hadisin: Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka…

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ruwaitowa daga Ubangijinsa cewa idan bawa ya aikata zunubi sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai ce: Bawana ya aikata zunubi, kuma ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, Ya suturtashi ya yafe masa, ko yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafarta masa. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Ya yi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana, sai ya aikata abin da ya so muddin dai cewa shi a duk lokacin da ya yi zunubi zai bar zunubin ya yi nadama, ya yi niyyar barin komawa a cikinsa, sai dai zuciyarsa tana rinjayarsa, sai ya afka a cikin zunubi karo na gaba, muddin dai yana aikata haka yana zunubi yana tuba, to, zan gafarta masa; domin cewa tuba yana rushe abin da ke kafinsa.

Koyarwar hadisin: Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN ZIKIRI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah