ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka Rakuminka? Karbi Rakuminka da kudink…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka Rakuminka? Karbi Rakuminka da kudink…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka R…

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما : «أنه كان يسير على جمل فأعيا، فأراد أن يُسَيِّبَهُ. فلحقني النبي صلى الله عليه وسلم فدعا لي، وضربه، فسار سيرا لم يَسِرْ مثله. ثم قال: بِعْنِيهِ بأُوقية. قلتُ: لا. ثم قال: بِعْنِيه. فَبِعْتُهُ بأوقية، واستثنيت حُمْلَانَهُ إلى أهلي. فلما بلغت: أتيته بالجمل. فنقدني ثمنه. ثم رجعت. فأرسل في إثري. فقال: أتَرَانِي مَاكستُكَ لآخذ جملك؟ خذ جملك ودراهمك، فهو لك».

Bayanin hadisin: ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka R…

Jabir ya kasance tare da Annabi a daya daga cikin yakunansa, kuma ya kaance yana kan Rakumi wanda ya rame, sai ya kaa tafiya da iya daidaita tafiyarsa da ayari, har cewa shi yaso ya kyale shi yai tafiyarsa shi kadai, sabida rashin amfaninsa kuma Annabi ya kasance sabida tausayinsa sa da Sahabbansa da kuma Al'ummasa yana tafiya ne a bayan Runduna don tausayawa rarrauna, da wanda ya gajiya da kuma wanda guzurinsa ya kare, sai ya gamu da Jabir yana kan Rakuminsa, sai yayi masa Addua kuma ya daki Rakumin, sai dukan mai girma ya zama jin kai da kuma karin karfi da taimako ga gajiyayyen Rakumi, sai ya fara tafiya tafiyar da bai taba yinta ba, sai Annabi sabida Karamcinsa da kyawawn Dabi'unsa da tausayawarsa ya so faranta ran Jabir da kuma daukarsa da Magana da zata dauke masa kewar tafiya, sai ya ce: to siyar mun da Rakumin da kimar Ukiyya to Jabir sai yai kwadayin falalar Allah kuma ya sani cewa babu tawaya a Adininsa da zai ki siyarwa Annabi Rakuminsa, domin wannan baya cikin biyayya ta wajibi, domin Umarnin bai zama na dole ba, kuma duk da haka Annabi ya kara tambayarsa da ya siyar masa da Ukiyya, kuma ya shardanta masa cewa zai ci gaba da hawa har zuwa gida Madina, ai Annabi ya yarda da sharadinsa da suka iso, sai ya zo masa da Rakumi, kuma ya bashi kudin yayin da ya koma sai ya aiko bayansa a kirawo shi kuma ya ce da shi, kana ganin na sayi Rakuminka don kwadayin in rabaka da shi? Dauki Rakuminka da kudinka duka na baka, kuma irin wannan ba abin Mamaki bane kan Karamcin Annabi da kuma halayyarsa da kuma tausasawarsa, kuma Annabi yana da irin wadan nan misalan manya a tarihinsa

Rukunan : FIƘHU NA MU'AMALAT · CINIKAYYA · SHARUƊA A CINIKI · SIRAR ANNABI · FIƘHU DA USULU · SIRA DA TARIHI · KEƁENCE-KEƁENCEN ANNABI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah