Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Yana daga sunna in ya auri budurwa: sai ya yi kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana,…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: «من السنة إذا تَزَوَّجَ البِكْرَ على الثَّيِّبِ: أقام عندها سبعا ثم قَسَمَ. وإذا تَزَوَّجَ الثَّيِّبَ: أقام عندها ثلاثا ثم قَسَمَ».
قال أبو قلابة:" ولو شِئْتُ لَقُلْتُ: إنَّ أَنَسًا رَفَعَهُ إلى النبي صلى الله عليه وسلم ».
Yana daga sunna in mutum ya auri budurwa ya kwana a dakinta har tsawon kwana bakwai don ya dauke mata kewa ya kuma saba da ita sannan ya wayar da kanta game da lamarin aure, don kasancewarta bakuwa a harkar aure, sannan kuma sai ya raba kwana. In bazawara ce ya kwana uku a wajenta, saboda karancin bukatarta akan budurwa cikin wadancan lamuran, wannan hukuncin ya zo ne cikin hadisin da ke da hukuncin dagawa zuwa ga Annabi, don kuwa masu rawaito hadisi in suka ce yana daga sunna, to sunnar Annabi suke nufi, ba ta wani ba, Duk hadisin da aka ce zuwa ga Annabi, ko an daukaka shi, to ana nufin an jingina shi zuwa ga Annabi
Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · AURE · FIƘHU DA USULU · ZAMANTAKEWA TSAKANIN MA'AURATA