Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
Bayanin hadisin: Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambata alahali yana huɗubar akan sadaka da kamewa daga roƙo akan minbari; sannan ya ce: Hannau maɗaukaki mai ciyarwa mai bayarwa shi ne nafi alheri kuma mafi soyuwa a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo.
Koyarwar hadisin: Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
- A cikinsa akwai falalar bayarwa da kuma ciyarwa a hanyoyin alheri da kuma zargin roƙo.
- A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma wadatuwa daga mutane, da kwaɗaitarwa akan kyawawan al'amura, da barin komabayansu, Allah Yana son kyawawan al'amura.
- Hannaye guda huɗu ne, su a falala kamar yadda yake tafe ne: Maɗaukakinsu mai ciyarwa, sannan mai kamewa daga karɓa, sannan mai karɓa ba tare da roƙo ba, sannan komkabayansu shi ne mai roƙo.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI
· ZAKKA
· CIYARWA
· FIƘHU DA USULU
· SADAKA TA NAFILA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad