Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin…
Musulunci > Ha > Hadith > Bidia > Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2
Rubutun hadisin: Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shek…
Bayanin hadisin: Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shek…
Sarkin musulmai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa idan kuka ji ni ina zantar da wani hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lallai cewa ni banayin alkunya bana yin jirwaye mai kama da wanka kuma bana yin tauriyya, kawai ina magana ne ɓaro-ɓaro, kuma a ce in faɗo daga sama shi ya fi sauƙi a gurina daga in zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ina yi masa ƙarya, idan na yi magana a abinda ke tsakanina da mutane to lallai cewa yaƙi ɗan yaudara ne, saboda haka zan iyayin alkunya ko in yi jirwaye mai kama da wanka ko in yi tauriyya, haƙiƙa na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wasu matasa zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru, masu raunin hankula, suna faɗin (magana daga) Alƙur'ani kuma suna yawaita karanta shi, zasu fita daga Musulunci kuma su ƙetare iyakokinsa kamar yadda kibiya take fita daga abinda aka harba, imaninsu ba ya wuce maƙogwaransu, a duk inda kuka haɗu da su to ku kashesu, domin cewa kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama.
Koyarwar hadisin: Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shek…
- Bayanin wani abu daga cikin siffofin Khawarij.
- A cikin hadisin akwai alama daga alamomin Annabta, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labarin shi.
- Halaccin yin tauriyya da jirwaye mai kama da wanka a cikin yaƙi, yaudara a cikin yaƙi tana kasancewa ne ta hanyar yin tauriyya, kuma tana kasancewa ta hanyar bazata, da makamancinsu, ba tare da warware alƙawari ba ko (warware) amintarwa ba, saboda zuwan hani akan hakan.
- Nawawi ya ce akan (ma'anar) (Suna faɗa daga mafi alherin zancen talikai) Ma'anarsa: A zahirin al'amari kamar faɗinsu: Babu wani hukunci sai na Allah, da makamancinsa daga kiransu zuwa Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
- Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa (Imaninsu ba ya ƙetare maƙogwaransu): Abin nufi cewa imani bai tabbata a cikin zukatansu ba; domin dukkan abinda ya tsaya a maƙogwaro bai ƙetare shi ba to ba ya kaiwa zuciya.
- Alƙali ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan cewa Kahawarij da makamantansu cikin 'yan bidi'a da tawaye a duk lokacin da suka yi wa shugaba tawaye suka saɓa ra'ayin jama'a suka raba kawunan mutane to ya wajaba a yaƙesu bayan an yi musu gargaɗi, an gabatar da uzuri garesu.
Rukunan :
BIDI'A
· FIƘHU NA IBADA
· JIHADI
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· Ahl-us-Sunnah's (Sunni) Stance on Religious Innovators
· Rulings of Terrorism, Assassinations, and Explosions
· Imani da Manzanni
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· KARAMOMIN WALIYYAI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad