‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakanins…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakanins…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da…

Bayanin hadisin: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkan mumini zai tsaya a gaban Allah a ranar lahira shi kaɗai, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi magana da shi ba tare da wani wasiɗa ba, kuma babu wani tafinta a tsakaninsu wanda zai fassara zancen, sai ya yi duba ɓangaren dama da hagu saboda tsananin firgici, wataƙila zai samu hanyar da zai gudu a cikinta dan ya tsira daga wutar dake gabansa. Idan ya yi duba a ɓangaren da ke damansa ba zai ga komai ba sai abinda ya aikata na aiki na gari Idan ya yi duba a hagunsa ba zai ga komai ba sai abinda ya gabatar na mummunan aiki, idan ya duba gabansa ba zai ga komai ba sai wuta, kuma babu abinda zaisa shi kauce mata dan babu makawa daga wucewa akan siraɗi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku sanya kariya tsakaninku da wuta da sadaka da aiki na gari, koda da wani sassauƙan abu ne kamar rabin dabino.

Koyarwar hadisin: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · ZAKKA · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · SADAKA TA NAFILA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah