Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita ida…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na zamantakewar iyali > Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita ida…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad

Hasan ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a k…

Bayanin hadisin: Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a k…

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - menene haƙƙin mata akan mijinta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wasu al'amura, daga cikinsu:

Na farko: Kada ka keɓanci kanka da abin ci banda ita; kai ka ciyar da ita a duk lokacin da ka ci abin ci.

Na biyu: Kada ka keɓanci kanka da tufatarwa da tufafi, kai ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), hak idan ka yi aiki kuma ka samu iko.

Na uku: Ba'a dukanta sai da wani sababi da buƙatuwa, idan ya buƙatu zuwa dukanta dan ladabtarwa ko dan barinta wasu farillai to sai ya zama duka ba mai sa rauni ba; kuma ba'a dukan fuska; domin cewa fuska ita ce mafi girman gaɓɓai kuma mafi bayyanarsu kuma ta ƙunshi wasu sasanni manya da gaɓɓai masu laushi.

Na huɗu: Kada ka yi zagi ko ka ce : Allah Ya munana fuskarki; kada ka danganta koda wani abu daga jikinta zuwa munin da shi ne kishiyar kyau; domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne wanda Ya suranta fuskar mutum da jikinsa, kuma Ya kyautata halittar kowane abu, zargin halitta yana komawa ne zuwa zargin Mahalicci tsarki ya tabbata ga Allah.

Na biyar: Kada ka ƙaurace sai a wurin kwanciya, kuma kada ka juya mata baya, kada ka juyar da ita zuwa wani gidan daban; wataƙila hakan a cikin abinda afkuwarsa yake sabawa ne daga ƙauracewa tsakanin miji da mata.

Koyarwar hadisin: Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a k…

Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · AURE · FIƘHU DA USULU · ZAMANTAKEWA TSAKANIN MA'AURATA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah