Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Alla…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن سَمُرَة بن جندبٍ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَحَبُّ الْكَلَامِ إِلَى اللهِ أَرْبَعٌ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، لَا يَضُرُّكَ بِأَيِّهِنَّ بَدَأْتَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi soyuwar zance a wurin Allah huɗu ne:
Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya.
Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai.
Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.
Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · SAKAKKUN ZIKIRAI · FALALOLI DA LADUBBA