Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
Bayanin hadisin: Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya zagi ɗan uwansa musulmi, kuma hakan yana daga fasiƙanci shi ne fita daga yi wa Allah ɗa'a da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma yaƙar musulmi ga ɗan uwansa musulmi yana daga ayyukan kafirci, sai dai hakan kafirci ne ƙarami.
Koyarwar hadisin: Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
- Wajabcin girmama mutuncin musulmi da jininsa.
- Girman lamarin zagin musulmi ba tare da wani haƙƙi ba; to mai zagin ba tare da wani haƙƙi ba fasiƙi ne.
- Zagin musulmi da yaƙarsa yana raunana imani kuma yana tauye shi.
- Sashin ayyuka ana ambatansu kafirci; koda basu kai ga kafirci babba mai fitarwa daga tafarkin Musulunci ba.
- Abin nufi da kafirci a nan kafirci ƙarami wanda ba ya fitarwa daga Addini da haɗuwar Ahlus Sunnah; domin Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya tabbatar da 'yan uwantaka ta imani ga muminai a halin yaƙi tsakaninsu da kuma jayayyarsu, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce; {Idan ƙungiyoyi biyu ta muminai suka yi faɗa to ku yi sulhu a tsakaninsu} zuwa faɗinSa; {Kaɗai muminai 'yan uwa ne}.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE ABIN ZARGI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah