Kunya tana daga imani
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Kunya tana daga imani
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Kunya tana daga imani
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا يَعِظُ أَخَاهُ فِي الْحَيَاءِ، فَقَالَ: «الْحَيَاءُ مِنَ الْإِيمَانِ».
Bayanin hadisin: Kunya tana daga imani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wani mutum yana yi wa wani ɗan uwansa nasihar cewa ya bar yawan kunya! sai ya bayyana masa cewa kunya tana daga imani, kuma ba ta zuwa sai da alheri.
Kunya ɗabi'a ce da take sa aikata mai kyau da barin mummuna.
Koyarwar hadisin: Kunya tana daga imani
- Abin da zai hana ka alheri ba a ambatonsa kunya, kai ana ambatonsa tsoro da gajiyawa da rauni da ragonta.
- Kunyar Allah - Mai girma da daukaka - tana kasancewa ne da aikata abubuwan da aka umarta, da barin abubuwan da aka hana.
- Kunyar ababen halitta tana kasancewa ne da girmamasu, da saukar da su masaukansu, da nisantar abin da zai munana a al'adance.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah