Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi…
Tirmizi ya ce Hadisi ne HasanAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ أَبِي ذَرٍّ، جُنْدُبِ بْنِ جُنَادَةَ، وَأَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ، مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «اتَّقِ اللَّهَ حَيْثُمَا كُنْت، وَأَتْبِعْ السَّيِّئَةَ الْحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقْ النَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA