Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
Bayanin hadisin: Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda aka haramtawa sauƙi to ba'a datar da shi ba a cikin al'amuran addini dana duniya haka da cikin abinda yake tasarrufi a cikinsa ga kansa, da kuma abinda yake tasarrufi a cikinsa tare da waninsa, to haƙiƙa an hana masa alheri gabaɗayansa.
Koyarwar hadisin: Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
- Falalar sauƙi da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da shi, da zargin tsanani.
- Sauƙi da shi ne aka samu tsarin alkairan duniya da lahira da yalwatuwar al'amuransu, a kwai kishiyar hakan a cikin tsanani.
- Sauƙi mai fitowane daga kyawawan ɗabi'u da zaman lafiya, shi kuma tsanani mai fitowane daga fushi da zafin zuciya, saboda hakane tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi yabo ga sauƙi kuma ya zurfafa a cikinsa.
- Sufyanus Sauri - Allah Ya yi masa rahama - ya cea almajiransa: Shin kun san menene sauƙi? shi ne ka sanya al'amura a bigiransu, tsanani a bigiransa, laushi a bigiransa, takobi a bigiranta, bulala a bigiranta.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah