Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi k…
عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «يَسِّرُوا وَلَا تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلَا تُنَفِّرُوا».
Bayanin hadisin: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi k…
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta.
Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.
Koyarwar hadisin: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi k…
- Wajibin dake kan mumini shi ne ya sanya wa mutane son Allah, ya kwadaitar da su alheri.
- Ya kamata ga mai kiran mutane zuwa ga Allah ya yi nazari cikin hikima a kan yadda zai isar da saƙon Musulunci zuwa ga mutane.
- Bushara tana haifar da farin ciki da karɓuwa da nutsuwa da abin da mai Da'awa ya ke gabatarwa ga mutane.
- Tsanantawa tana haifar da ƙyama da kuma juya baya da sanya shakku a maganar mai Da’awah.
- Yalwatuwar rahamar Allah ga bayinSa, da cewa Ya yardar musu da addini mai sauƙi da Shari’ah mai rangwame.
- Sauƙi da aka yi umarni da shi, shi ne wanda Shari’a ta zo da shi.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah