Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na zamantakewar iyali > Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’…
Bayanin hadisin: Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana miji ya ki matarsa ƙin da zai kai zuwa ga zalinci da barinta da bijire mata; Domin mutum an halicce shi ne akan tawaya, idan ya ki wata mummunar ɗabi'a daga gareta, to zai samu wata kyakkyawar ɗabi'ar a tare da ita; sai ya yarda da mai kyan da ta dace da shi, kuma ya yi haƙuri akan wadda bai yarda ba ta munanar, abinda zai sa shi ya yi haƙuri kada ya ki ta ƙiyayyar da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita.
Koyarwar hadisin: Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’…
- Kiran mumini zuwa adalci da hukuncin hankali a kowanne saɓanin da ya faru tare da matarsa, da rashin komawa zuwa hukuncin zuciya da fusatar wani ɗan lokaci.
- Sha'anin mumini kada ya ki mumina ƙiyayya baki ɗaya da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita, kai abinda ya kamata akansa ya kau da kai daga abinda yake ƙi dan abinda yake so.
- Kwaɗaitarwa akan kyakkyawan mu'amala da zamantakewa tsakanin ma'aurata.
- Imani mai kira ne ga kyawawan ɗabi'u, mumini da mumina ba sa kaɗaitaka daga kyawawan ɗabi'u; to imani yana lazimtar samun ɗabi'u ababen yabo a cikinsu.
Rukunan :
FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI
· AURE
· HUKUNCE-HUKUNCEN MATA
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma