Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yak…

عن النُّعمان بن بَشير رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ -وَأَهْوَى النُّعْمَانُ بِإِصْبَعَيْهِ إِلَى أُذُنَيْهِ-: «إِنَّ الْحَلَالَ بَيِّنٌ وَإِنَّ الْحَرَامَ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا مُشْتَبِهَاتٌ لَا يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ، وَمَنْ وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِي الْحَرَامِ، كَالرَّاعِي يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ، أَلَا وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمًى، أَلَا وَإِنَّ حِمَى اللهِ مَحَارِمُهُ، أَلَا وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً، إِذَا صَلَحَتْ صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ فَسَدَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، أَلَا وَهِيَ الْقَلْبُ».

Bayanin hadisin: Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yak…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: Bayyanannen halal, da bayyanannen haram, da al'amura masu rikitarwa waɗanda hukuncinsu ba a bayyane yake ba ta bangaren halacci da haramci, da yawa daga mutane basa sanin hukuncinsu.

Wanda ya bar waɗannan abubuwan masu rikitarwa gareshi, to, addininsa ya kuɓuta ta hanyar nisanta daga fadawa a cikin haram, kuma mutuncinsa ya kuɓuta daga zancen mutane da abin da za su dinga aibatashi a kansa saboda aikata wannan abin rikitarwar. Wanda bai nisanci shubuhohi ba, to, haƙiƙa ya kai kansa ko dai ga faɗawa a cikin haram, ko aibatawar mutane ga mutuncinsa. Kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don ya bayyana halin wanda yake aikata shubuhohi, kuma cewa shi kamar mai kiwo ne da yake kiwon dabbobinsa kusa da ƙasar da mai ita ya sa mata shinge, dabbobin mai kiwon sun kusa su yi kiwon a cikin wannan shingen don kusancinsu gareshi, to, haka nan wanda yake aikata a bin da a cikinsa akwai shubha, to, shi da wannan ɗin yana kusantowa ga haram, kuma yana kusa da ya afka cikinsa. Bayan wannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa a cikin jiki akwai wata tsoka (ita ce zuciya) jiki yana gyaruwa da gyaruwarta, kuma yana ɓaci da ɓacinta.

Koyarwar hadisin: Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yak…

Rukunan : USUL - ALFIƘH · HUKUNCIN SHARI'A · FALALOLI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · FALALOLIN AYYUKAN ZUCIYA · TSARKAKE ZUKATA · FIƘHU DA USULU · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah