‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana gom…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na zamantakewar iyali > ‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana gom…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: ‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba,…

Bayanin hadisin: ‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba,…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani ga mai idda (takaba) daga barin ado na tirare da kwalli da kayan ado da kyawawan kayan sawa ga mamaci sama da kwana uku, uba ne ko ɗan'uwa ko ɗa ko wasunsu, sai ga miji kawai wata huɗu da kwana goma, kuma alokacin iddarta (takaba) ga miji, kar ta sanya dukkanin rinannun tufafi dan yin ado sai tufafin asb, shi ne tufa na Yaman wanda ake rinawa kafin a saƙa shi, kuma kada ta sa kwalli a ido dan yin ado, kada ta shafa tirare mai ƙanshi da waninsu, sai dai idan ta yi wankan haila, sai ta shafa wani gutsire ƙarami na tiraren ƙusɗ ko azafar, su wasu nau’uka ne sanannu na tiraren wuta, basu zama daga manufar shafa tirare ba, an yi rangwami a cikinsa ga wacce ta yi wankan daukewar al’ada dan kawar da warin da ba'a so, da zata bibiyi gurbin jini da shi a acikin farji ba dan shafa tirare ba.

Koyarwar hadisin: ‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba,…

Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · IDDA · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah