Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da z…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da z…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu…
Bayanin hadisin: Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Kirista ko waninsu (ba zai ji) kiran Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya isa zuwa gare shi ba, sannan ya mutu bai yi imani da shi ba sai ya zama daga 'yan wuta yana madawwami a cikinta har abada.
Koyarwar hadisin: Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu…
- Gamewar sakon Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa dukkanin halittu, da wajabcin binsa, da shari'arsa ta shafe dukkanin shari'o'i.
- Wanda ya kafirce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi - ikirarins na imani da waninsa daga Annabawa - tsira da aminci ya tabbata agare su baki daya - ba zai amfanar da shi da komai ba.
- Wanda bai ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, kuma sakon musulunci bai isa zuwa gare shi ba to shi yana da uzuri, al'amarinsa a lahira yana ga Allah - Madaukakin sarki -.
- Amfanuwa da musulunci yana tabbata koda kafin mutuwa ne, koda a halin tsananin rashin lafiya ne, muddin dai rai bai kai makogwaro ba.
- Inganta Addinin kafirai - daga cikinsu akwai yahudawa da kiristoci - kafirci ne.
- Ambaton yahudawa da kiristoci - a cikin hadisin - dan fadakarwa ne akan wasunsu; hakan domin cewa yahudawa da kiristoci suna da littafi, idan hakan ya zama sha'aninsu, to wasunsu daga wadanda ba su da littafi ya fi cancanta, dukkaninsu shiga Addininsa da biyayya gareshi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zama dole akansu.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· Imani da Manzanni
· ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma