Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani mutum daga mutane da zai ketare matsayar hisabi a ranar Alkiyama zuwa aljanna ko wuta ba har sai an tambaye shi game da wasu al'amura:
Na daya: Rayuwarsa a me ya karar da ita?
Na biyu: Iliminsa shin ya neme shi ne saboda Allah? kuma ya yi aiki da shi? kuma shin ya isar da shi ga wanda ya cancance shi?
Na uku: Dukiyarsa daga ina ya samota shin daga halal ne ko daga haram? kuma a me ya ciyar da ita a abinda zai yardar da Allah ne, ko a abinda zai fusatar da Shi?
Na hudu: Jikinsa da karfinsa da lafiyarsa da samartakarsa a me ya yi da shi ya kuma aiwatar da shi?
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Ranar Lahira · RAYUWAR LAHIRA