Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi gir…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi gir…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a…

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الذَّنْبِ أَعْظَمُ عِنْدَ اللهِ؟ قَالَ: «أَنْ تَجْعَلَ لِلهِ نِدًّا وَهُوَ خَلَقَكَ» قُلْتُ: إِنَّ ذَلِكَ لَعَظِيمٌ، قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «وَأَنْ تَقْتُلَ وَلَدَكَ؛ تَخَافُ أَنْ يَطْعَمَ مَعَكَ» قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «أَنْ تُزَانِيَ حَلِيلَةَ جَارِكَ».

Bayanin hadisin: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a…

Antambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga mafi girman zunubai sai ya ce: Mafi girmansu babbar shirka, ita ce ka sanya tamka ko kini ga Allah a AllantakarSa ko UbangidantakarSa ko sunayenSa da siffofinSa, wannan laifin Allah - Madaukakin sarki - ba ya gafartashi saida tuba, idan mai aikata shi ya mutu akansa to shi madawamine a cikin wuta. Sannan mutum ya kashe dansa dan tsoron ya ci tare da shi, kashe rai kuwa haramun ne, saidai zunubinsa yana girmama idan wanda aka kashe din yana da alaka ta jini da wanda ya yi kisan, kuma zunubinsa yana girmama yayin da manufar wanda ya yi kisan ta zama dan tsoron ya yi tarayya da wanda aka kashe din ne a arzzikin Allah. Sannan mutum ya yi zina da matar makocinsa shi ne ya yi kokarin rudar da matar makocinsa har ya yi zina da ita ta mika wuya gare shi . Zina haramun ce , saidai zunubinta yana girmama idan wacce aka yi zinar da ita matar makoci ce wanda shari'a ta yi wasicci da kyautatawa zuwa gareshi da yi masa kirki da kayauta zama da shi.

Koyarwar hadisin: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin Rububiyya

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.7 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah