Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirar…
Bayanin hadisin: Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirar…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta sashin abinda ke cikin ranar alƙiyama, kuma mutane za'a tarasu bayan tashinsu daga ƙaburburansu dan yin hisabi, kuma cewa halinsu zasu zama marasa takalma, tsirara babu tufafi, marasa kaciya kamar ranar da iyayensu suka haifesu, yayin da Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ji hakan sai ta ce tana mai mamaki: Ya Manzon Allah ! maza da mata baki ɗayansu sashinsu yana kallon sashi?! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa: Sha'anin tsayuwar da taruwa bayan tashi daga mutuwa a cikinsa akwai tsorace-tsoracen da zai ɗauke hankalin mutane da idanuwansu daga kallan al'aurori.
Koyarwar hadisin: Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirar…
- Bayanin tsorace-tsoracen ranar Lahira, kuma cewa mutum a wannan ranar wani abu ba zai shagaltar da shi daga hisabinsa ba haka nan ayyukansa.
- Karfafawa cewa mutum ba zai afka cikin saɓo ba sai dai a halin rafkana; dan da zai tina girman wanda ya saɓawa ko uƙubarSa da bai rafkana ba daga tinaShi da kuma gode maSa da kyakkyawan bautarSa ko da ƙiftawar ido, saboda haka zaka ga ma'abota taron alƙiyama sun shagalta da kawunansu sashinsu ba ya kallon sashi.
- Tsananin kunyar mata a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, wannan Nana A'isha ce - Allah Ya yarda da ita - tana tambaya cikin kunya lokacin da ta ji cewa za'a tashi halitta tsirara maza da mata.
- Sindi ya ce: Kowanne mutum ya shagalta da al'amarinsa kuma bai san halin ɗan'uwansa ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar sha'aninsa ya wadace shi} [Abasa: 37]. Babu wani da zai iya juyawa zuwa ga al'aurar wani.
- Kaciya: Ita ga namiji ita ce: Yanke fatar da ta rufe hashafa, ta mace kuma ita ce: Yanke fatar da ke saman bigiren da azzakari yake shiga ya yi kama da ƙahon zakara.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR LAHIRA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma