Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kum…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kum…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «قَالَ اللَّهُ: كَذَّبَنِي ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، وَشَتَمَنِي وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: لَنْ يُعِيدَنِي، كَمَا بَدَأَنِي، وَلَيْسَ أَوَّلُ الخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَيَّ مِنْ إِعَادَتِهِ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا وَأَنَا الأَحَدُ الصَّمَدُ، لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لِي كُفْؤًا أَحَدٌ».

Bayanin hadisin: Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyanawa acikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya sanar game da mushrikai da kafirai cewa su suna karyataShi suna siffantaShi da tawaya da aibobi, kuma hakan bai kamacesu ba.

Amma karyatawar da suka yi wa Allah: Ita ce riyawarsu cewa Allah Ba zai dawo da su bayan mutuwarsu ba akaro na gaba, kamar yadda Ya haliccesu tun afarko da ba su, sai ya yi musu raddi da cewa Wanda Ya fari halitta daga babu mai iko ne akan dawo dasu kai hakan mafi sauki ne ma, duk da al'amarin dangane da Allah daidai ne halitta da dawowa, Allah Mai iko ne akan dukkan komai.

Amma aibantawar: To fadinsu: Cewa Shi Yana da Da, sai ya yi musu raddi da cewa Shi ne daya Kwal, Mai kadaituwa da dukkanin cika a sunayenSa da siffofinSa da ayyukanSa, abin tsarkakewa daga kowacce tawaya da aibi, abin nufi da bukata wanda baYa bukatuwa ga wani, kuma kowa mai bukatuwane gareShi, kuma bai zama mahaifi ga wani ba, kuma baShi da wani Da, kuma baShi da tamka, tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka.

Koyarwar hadisin: Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah