Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sann…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sann…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan s…
Bayanin hadisin: Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan s…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin farkon jama'a ta muminai waɗanda zasu shiga aljanna fuskokinsu suna kan surar wata daren goma sha huɗu a haske, sannan masu biye musu suna kan surar tauraro mafi tsananin haske, kuma suna da wasu siffofin cika inda ba sa fitsari ba sa bahaya, kuma ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abubuwan taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski. Kuma abin kunna tiraren wutarsu yana tada ƙanshi mafi daɗin ƙanshin tirare kuma mafi ƙanshin tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inu, halittarsu akan halittar mutum ɗaya ne akan surar babansu Annabi Adam a tsawo da kuma halitta; tsawon jikinsa zira'i sittin ne a sama.
Koyarwar hadisin: Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan s…
- Bayanin siffar 'yan aljanna, kuma cewa su suna da fifiko a cikinta gwargwadan darajojinsu da kuma ayyukansu.
- Anafni da tashbihi (karantawa) don kusanto da ma'anoni da kuma sharhinsu.
- AlƘurɗubi ya ce: Za'a iya cewa to wace buƙata suke da ita na taje kai alhali su matasa ne kuma gashinsu ba ya datti? Kuma wace buƙata ce da su ga tiraren wuta alhali ƙanshinsu ya fi almiski? Ya ce: Za'a amsa da cewa ni'imar 'yan aljanna na ci da sha da tufafi da tirare badan jin raɗaɗin yunwa ba ne ko ƙishirwa ko tsiraici ko wari, kawai su daɗi ne a jere da ni'imomi a jere, kuma hikima a cikin hakan cewa su suna ni'imtuwa da nau'in abinda suka kasance suna ni'imtuwa da shi ne a duniya.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ILIMIN AƘIDA
· SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA
· FALALOLI DA LADUBBA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR LAHIRA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah