Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah …

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah …

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye A…

عَنْ أَبِي العَبَّاسِ، عَبْدِ الله بْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: كُنْت خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: «يَا غُلَامِ! إنِّي أُعَلِّمُك كَلِمَاتٍ: احْفَظِ اللَّهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ الله تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاَللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الأُمَّةَ لَوْ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَنْفَعُوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ لَكَ، وَإِنِ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَضُرُّوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ عَلَيْكَ؛ رُفِعَتِ الأَقْلَامُ، وَجَفَّتِ الصُّحُفُ».
وَفِي رِوَايَةِ غَيْرِ التِّرْمِذِيِّ: «احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ أَمَامَكَ، تَعَرَّفْ إلَى اللهِ فِي الرَّخَاءِ يَعْرِفْكَ فِي الشِّدَّةِ، وَاعْلَمْ أَنَّ مَا أَخْطَأَكَ لَمْ يَكُنْ لِيُصِيبَكَ، وَمَا أَصَابَك لَمْ يَكُنْ لِيُخْطِئَكَ، وَاعْلَمْ أَنَّ النَّصْرَ مَعَ الصَّبْرِ، وَأَنْ الفَرَجَ مَعَ الكَرْبِ، وَأَنَّ مَعَ العُسْرِ يُسْرًا».

Bayanin hadisin: Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye A…

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai da su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, domin haƙiƙa Shi Allah Shi kaɗai ne wanda Yake amsawa masu roƙo. Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara shi a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka Ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarSa da saninSa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta shi. Kuma cewa wanda ya kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa; to Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana gaban bawa, Yana sanin abin da yake a kansa, kuma zai taimake shi Ya kuma ƙarfafe shi. Kuma lallai mutum idan ya bi Allah a cikin wadata to lallai cewa Allah zai sanya masa yayewa da mafita a lokacin tsanani, kuma kowane bawa ya yarda da abin da Allah Ya ƙaddara masa na alheri da na sharri. Kuma ya lazimci haƙuri a lokacin tsanani da kuma jarrabawa, domin haƙuri mabuɗin yaye baƙin ciki ne, kuma baƙin ciki idan ya yi tsanani sai yayewa tazo daga Allah, kuma cewa tsanani idan ya faru Allah sai Allah Ya biye masa da sauƙi.

Koyarwar hadisin: Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye A…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Imani da Hukuncin Allah da Ƙaddara · Kaɗaita Allah cikin Rububiyya

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah