Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sa…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sa…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَة رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إنَّ اللَّهَ تَعَالَى قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقْد آذَنْتُهُ بِالحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إلَيَّ عَبْدِي بِشَيْءٍ أَحَبَّ إلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وما يَزَالُ عَبْدِي يَتَقَرَّبُ إلَيَّ بِالنَّوَافِلِ حَتَّى أُحِبَّهُ، فَإِذَا أَحْبَبْتُهُ كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطِشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي بِهَا، وَإِنْ سَأَلَنِي لَأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنْ اسْتَعَاذَنِي لَأُعِيذَنَّهُ».

Bayanin hadisin: Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari a cikin hadisi Ƙudusi cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Duk wanda ya cutar da wani waliyyi daga cikin waliyyaiNa ya fusatar da shi ya ƙishi to haƙiƙa na sanar da shi kuma na bayyanar da adawata gare shi. Waliyyi shi ne; Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abin dake ga bawa na imani da taƙawa rabonsa na soyayyar Allah take kasancewa gare shi, kuma musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu mafi soyuwa gare shi daga abin da ya wajabta masa na aikata ayyukan ɗa'a da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana neman kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; har sai ya samu soyayyar Allah, idan Allah Ya so shi sai Allah Ya zama mai daidaita masa waɗannan gaɓɓan guda huɗu. Zai daidaita shi a cikin jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi. Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ƙafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani ƙoƙari ba sai abin da a cikinsa akwai alheri. A tare da hakan idan ya roƙi Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roƙa, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro.

Koyarwar hadisin: Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah