‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > ‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa

Wanda ya ruwaito hadisin: Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shi

Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da…

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي الخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ».

Bayanin hadisin: ‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.

Koyarwar hadisin: ‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah