Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumin…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · Kaɗaita Allah cikin Rububiyya · ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI · Yankin Imani · KAFURCI