ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskar…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskar…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne Ya Rawaito shi

Hasan ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina nema…

Bayanin hadisin: ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina nema…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga masallaci zai ce: (Ina neman tsarin Allah Mai girma) Ina neman tsari ina fakewa ga Allah da kuma siffofinSa (Da fuskarSa mai kyauta) Mai kyauta Mai bayarwa, (Da sarautarSa) RinjayenSa da ikonSa da rinjayenSa akan wanda ya yi nufi daga halittarSa (Madawwami) na tun fi azal na har abada (Daga Shaiɗan abin jefewa) Abin nisantarwa abin korewa daga rahamar Allah, Wato; Ya Allah Ka kiyayeni daga wasiwasinsa da halakarwarsa da tsarinsa da haɗarinsa da ƙawacensa da ɓatarwarsa, domin shi ne sababi a ɓatarwa mai sa halakarwa da jahilci, Aka cewa Abdullahi ɗan Amr "Shin shike nan?" Wato: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wannan kadai? Ya ce: Eh.

Idan mai shiga masallaci ya faɗi wannan addu'ar; Shaiɗan zai ce : Haƙiƙa an kiyaye ran wannan mai shigowar daga gareni dukkanin lokaci, yininsa da darensa.

Koyarwar hadisin: ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina nema…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ILIMIN AƘIDA · ZIKIRAI NA SHIGA DA FITA DAGA MASALLACI · FALALOLI DA LADUBBA · IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah