Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai b…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai b…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa,…
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى تُقَاتِلُوا اليَهُودَ، حَتَّى يَقُولَ الحَجَرُ وَرَاءَهُ اليَهُودِيُّ: يَا مُسْلِمُ، هَذَا يَهُودِيٌّ وَرَائِي فَاقْتُلْهُ».
Bayanin hadisin: Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa,…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba zata tsayaba har sai musulmi da yahudawa sun yi yaki, Har idan bayahude ya gudu bayan dutse dan ya buyarwa musulmi; Allah zai sa dutsen ya yi magana ya kira musulmin: Da cewa akwai bayahude a bayansa har ya zo dan kashe shi.
Koyarwar hadisin: Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa,…
- Bada labarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wasu daga abubuwan dake boye da masu zuwa, yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya tsinkayar da shi, to shi zai afku babu makawa.
- Yaki tsakanin musulmai da yahudawa a karshen zamani, kuma wannan yana daga alamomin Alkiyama.
- Wanzuwar addinin Musulunci har zuwa ranar Alkiyama, da nasararsa akan addinai gaba daya.
- Taimakon Allah ga musulmai akan makiyansu, daga wannan akwai sanya dutse ya yi magana a karshen zamani.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR BARZAHU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa