Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a ciki…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa akan kusancin saukar (Annabi) Isa dan Nana Maryam - aminci ya tabbata agare shi - dan ya yi hukunci a tsakanin mutane da adalci da shari'ar Annabi muhammadu, kuma shi zai karya gicciyayye (kros) wanda kiristoci suke girmama shi, kuma Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai kashe alade, kuma cewa shi aminci ya tabbata agare shi zai sarayar da jiziya zai dora mutane gaba dayansu a shiga Addinin Musulunci. Kuma dukiya za ta yawaita wani ba zai karbeta ba; dan yawanta, da wadatuwar kowa da abinda ke hannunsa, da saukar albarka da malalowar alkairai.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · DA'AWA ZUWA GA ALLAH · GAMEWAR ADDININ MUSULUNCI · DA'AWA DA HISBA · Imani da Manzanni · Imani da Ranar Lahira · ANNABAWA DA MANZANNI MAGABATA AMINCI A GARESU · ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI · RAYUWAR BARZAHU