To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a ci…
Musulunci > Ha > Hadith > Ladubba na sharia > To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a ci…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah a…
Bayanin hadisin: To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah a…
Wasu daga cikin sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka ce: Lallai mu mun kasance muna ci amma bama ƙoshi.
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.
Koyarwar hadisin: To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah a…
- Haɗuwa a abinci da kuma ambatan Allah a lokacin ci sababi ne na samun albarka a cikin abinci, da kuma ƙoshi daga cinsa.
- Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.
- Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.
- Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN CI DA SHA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah