Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ أَبِي لَيْلَى قَالَ: لَقِيَنِي كَعْبُ بْنُ عُجْرَةَ، فَقَالَ: أَلاَ أُهْدِي لَكَ هَدِيَّةً؟ إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَيْنَا، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَدْ عَلِمْنَا كَيْفَ نُسَلِّمُ عَلَيْكَ، فَكَيْفَ نُصَلِّي عَلَيْكَ؟ قَالَ: «فَقُولُوا: اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ».
Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · LADUBBA NA SHARI'A · LADUBBAN MALAMI DA MAI KOYON ILILMI · FIƘHU DA USULU · ZIKIRAN SALLAH · FALALOLI DA LADUBBA