Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya…
عن أنس بن مالك رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ لَا يَرُدُّ الطِّيبَ.
Bayanin hadisin: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya…
Ya kasance daga cikin karantarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya ƙin karɓar turare, yana karɓarsa domin yana da sauƙin ɗauka, kuma yana da ƙamshi.
Koyarwar hadisin: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya…
- Mustahabbacin karɓar kyautar turare, domin babu wata wahala wurin ɗaukarsa, babu damuwa wurin karɓarshi
- Cika da kyakkyawan halin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wurin ƙin karɓar turare da kuma karɓar kyauta daga wanda ya yi masa.
- Kwaɗaitarwa a kan amfani da turare.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN ZIYARA DA NA NEMAN IZINI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye