Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tar…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tar…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi…
Bayanin hadisin: Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya tsoratar akan wasu ayyukan mutanen Jahiliyya, sai ya ce: Ba ya tare da mu:
Na farko: Wanda ya mari kundukuki (kumatu) an keɓanci kundukuki dan kasancewarsa shi ne galibi a hakan, inba haka ba marin sauran fuska yana shiga cikin hanin.
Na biyu: Yaga abnida ake buɗewa daga tufa dan kai ya shiga cikinsa saboda tsananin baƙin ciki.
Na uku: Yin kururuwa irin ta mutanen Jahiliyya kamar ihu da kaico da halaka da kukan mutuwa da wanin hakan.
Koyarwar hadisin: Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi…
- Wannan narkon a cikin hadisin yana nuni akan cewa waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.
- Wajabcin haƙuri akan masifa, da haramta fushi akan ƙaddarorin Allah masu raɗaɗi, da bayyanar da hakan: Da kukan mutuwa ko aske kai ko yaga riga ko wanin hakan.
- Haramcin kwaikwayon Jahiliyya da al'amuransu waɗanda mai shari'antawa bai tabbatar da su ba.
- Babu laifi akan damuwa da hawaye, shi ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah - Maɗaukakin sarki -, kawai shi tausayi ne Allah Ya sanya shi a cikin zukatan makusanta da masoya.
- Yarda da hukuncin Allah ya wajaba akan musulmi, idan bai yarda ba to haƙuri wajibi ne a kansa.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· MAS'ALOLIN JAHILIYYA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah