Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallata…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallata…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburbura…
Bayanin hadisin: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburbura…
Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.
Koyarwar hadisin: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburbura…
- Wannan yana daga wasiyyoyinsa na ƙarshe daga abinda yake nuni akan muhimmancinsu da kuma kulawa da su.
- Hani mai ƙarfi, da haramci mai tsanani daga riƙon ƙaburbura masallatai, da nufar yin sallah a wurinsu banda sallar jana'iza; to hakan hanya ce zuwa girmama mamacin da kuma ɗawafi a ƙabarinsa da shafa ƙinshiƙansa da kiran sunansa, kuma dukkanin wannan yana daga shirka da kuma hanyoyinta.
- Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama ƙaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa ga shirka.
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kiyaye Annabinsa - tsira da amincin su tabbata agare shi - da ayi shirka a wurin ƙabarinsa, sai ya cusawa sahabbansa da waɗanda ke bayansu su kiyaye ƙabarinsa da kada a fito da shi.
- Aikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kwaɗayinsu akan Tauhidi.
- Hani daga kamanceceniya da Yahudawa da Nasara, da kuma gini akan ƙaburbura yana daga al'adunsu.
- Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· JANA'IZA
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· ZIYARAR MAƘABARTA
· IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
· Kaɗaita Allah cikin bauta
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad