Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِعَمِّهِ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، أَشْهَدُ لَكَ بِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ»، قَالَ: لَوْلَا أَنْ تُعَيِّرَنِي قُرَيْشٌ، يَقُولُونَ: إِنَّمَا حَمَلَهُ عَلَى ذَلِكَ الْجَزَعُ لَأَقْرَرْتُ بِهَا عَيْنَكَ. فَأَنْزَلَ اللهُ: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ } [القصص: 56].
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi:
Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.
Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN TAUHIDI · ILIMIN AƘIDA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Hukuncin Allah da Ƙaddara · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · MUSULUNCI