Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wan…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wan…

Wanda ya ruwaito hadisin: Ibnu Majah ne ya ruwaito shi

Ingantacce ne ta wani bangaren

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

عَنْ زِيَادِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه قَالَ: ذَكَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَيْئًا، فَقَالَ: «ذَاكَ عِنْدَ أَوَانِ ذَهَابِ الْعِلْمِ» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَكَيْفَ يَذْهَبُ الْعِلْمُ، وَنَحْنُ نَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَنُقْرِئُهُ أَبْنَاءَنَا وَيُقْرِئُهُ أَبْنَاؤُنَا أَبْنَاءَهُمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ؟ قَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ زِيَادُ، إِنْ كُنْتُ لَأُرَاكَ مِنْ أَفْقَهِ رَجُلٍ بِالْمَدِينَةِ، أَوَلَيْسَ هَذِهِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَى يَقْرَؤونَ التَّوْرَاةَ وَالْإِنْجِيلَ، لَا يَعْمَلُونَ بِشَيْءٍ مِمَّا فِيهِمَا؟!».

Bayanin hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.

Koyarwar hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

Rukunan : FALALOLI · FALALAR ILIMI · ILIMIN AƘIDA · FALALOLI DA LADUBBA · Merit and Significance of Knowledge · Imani da Ranar Lahira · RAYUWAR BARZAHU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah