Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Alla…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ أَنْظَرَ مُعْسِرًا، أَوْ وَضَعَ لَهُ، أَظَلَّهُ اللهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تَحْتَ ظِلِّ عَرْشِهِ يَوْمَ لَا ظِلَّ إِلَّا ظِلُّهُ».
Annabi - tsira da amincin Allah - su tabbata agare shi - ya ba da labari cewa wanda ya saurarawa wanda ake bi bashi, ko ya sarayar masa daga bashinsa, to, sakamakonsa: shi ne Allah Zai inuwantar da shi ƙarƙashin al-Arshinsa a ranar Alƙiyama, wanda rana zata kusanto kawunan bayi a cikinta, kuma zafinta zai tsananta akansu. Babu wanda zai samu wata inuwa sai wanda Allah Ya inuwantar da shi.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Ranar Lahira · RAYUWAR LAHIRA