Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka a…
Bayanin hadisin: Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka a…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin mafarki ya gan shi a cikin aljanna, sai ya cewa Bilal Ibnu Rabah: Bani labarin mafi kwaɗayin aikin nafilar da ka aikata shi a cikin Musulunci? Domin ni na ji ƙarar takalmanka a hankali lokacin da kake motsasu kana tafiya a gabana a cikin aljanna. Bilal ya ce: Ban aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a wurina sai dai cewa ni ban taɓa yin kari (hadasi) ba da daddare ko da rana ba face sa na yi alwala, sannan na yi sallah saboda Ubangijina, ta nafilfili kai tsaye abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar
Koyarwar hadisin: Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka a…
- Falalar aikin da Bilal - Allah Ya yarda da shi - ya yi nuni a kansa, shine sallah a duk lokacin da mutum ya yi tsarki ya yi alwala, kuma shi yana daga cikn mafi kwaɗayin ayyuka kuma sababi na shiga aljanna.
- An so yin sallah bayan kowace alwala.
- Tambayar (mutum) wanda ake koyi da shi ko mai tarbiyya game da aikin almajirinsa; dan ya kwaɗaitar da shi akan tabbata a kansa idan ya kasance mai kyau ne, inba haka ba to sai ya hana shi.
- Shaidar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Bilal - Allah Ya yarda da shi - da cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
- Wannan tambayar a lokacin sallar Asuba ce, a cikin wannan akwai nuni cewa hakan ya faru ne a cikin mafarki daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafarkin Annabawa gaskiya ne.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· SALLAR NAFILA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR LAHIRA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah