Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da ab…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da ab…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu,…

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ أَهْلُ الْكِتَابِ يَقْرَؤُونَ التَّوْرَاةَ بِالْعِبْرَانِيَّةِ، وَيُفَسِّرُونَهَا بِالْعَرَبِيَّةِ لِأَهْلِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تُصَدِّقُوا أَهْلَ الْكِتَابِ وَلَا تُكَذِّبُوهُمْ، وَقُولُوا: {آمَنَّا بِاللهِ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْنَا} [البقرة: 136] الْآيَةَ».

Bayanin hadisin: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu,…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar da al'ummarsa daga ruduwa da abunda mazowa littafi suke ruwaitowa daga littattafansu, Yayin da Yahudawa suka kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna karanta Attaura da harshen ibirananci, shi ne harshen Yahudawa, kuma suna fassarata da larabci, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, wannan a cikin abinda ba'a gane gaskiyarsa daga karyarsa; Wannan domin cewa Allah - Madaukakin sarki - Ya umarcemu mu yi imani da abinda aka saukar agaremu na Alkur’ani , da abinda aka saukar garesu na littafi, saidai cewa shi babu wata hanya garemu zuwa musan ingancin abinda suke hakaitowa daga wadancan littattafan da kuma mara kyansa, idan abinda zai bayyana gaskiyarsa daga karyarsa bai zo a shari'armu ba, Sai mu tsaya, Ba zamu gasgata su ba; dan kar mu zama abokanan tarayya tare dasu a cikin abinda suka canza shi, kuma kada mu karyatasu; watakila zai iya zama ingantacce, sai mu zama masu musun abinda aka umarcemu da mu yi imani da shi. Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni mu ce: {Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne}. [Al-Baqara: 136].

Koyarwar hadisin: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu,…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · Rules and Principles of Exegesis · ILIMIN AƘIDA · IMANI DA LITATTAFAI · Pre-Islamic Scriptures

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah