Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne?…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بِن مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ العَمَلِ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «الصَّلاَةُ عَلَى وَقْتِهَا»، قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الوَالِدَيْنِ» قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ» قَالَ: حَدَّثَنِي بِهِنَّ، وَلَوِ اسْتَزَدْتُهُ لَزَادَنِي.
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya.
Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FALALOLI · FALALOLIN AYYUKA NAGARI · FIƘHU DA USULU · FALALAR SALLAH · FALALOLI DA LADUBBA